Pogba fitatcen dan wasa ne - Mourinho

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United za ta fafata da Southampton a wasa na biyu a gasar Premier

Kociyan Manchester United, Jose Mourinho, ya ce Paul Pogba, yana cikin fitattun 'yan wasan da suka yi fice a wasan tsakiya a tamaula a duniya.

Sai dai kuma kociyan ya ce dan kwallon zai yi gwagwarmaya wajen lashe lambar yabo ta kashin kansa, saboda rashin cin kwallaye wanda zai iya kawo masa tsaiko.

Pogba dan wasan tawagar Faransa ya koma United kan kudi fan miliyan 89, a matsayin wanda aka saya mafi tsada a tarihi a duniya.

Manchester United za ta karbi bakuncin Southampton a wasa na biyu na cin kofin Premier a ranar Juma'a.

Labarai masu alaka