Iheanacho ya tsawaita zamansa a Man City

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kelechi Iheanacho ya ci wa City kwallaye 14 a kakar da aka kammala

Dan wasan tawagar Nigeria, Kelechi Iheanacho, ya sabunta yarjejeniyar ci gaba da buga wa Manchester City tamaula zuwa shekara biyu.

Dan kwallon mai shekara 19, ya ci wa City kwallaye 14 a kakar wasannin da ta wuce, koda yake wasanni 25 daga 36 da ya yi ba da shi ake fara tamaula ba.

Sabon kociyan City, Pep Guardiola ne ya amince da Iheanacho ya ci gaba da murza-leda a Ettihad.

Dan kwallon shi ne na uku a yawan ci wa kungiyar kwallaye, bayan Sergio Aguero da Kevin de Bruyne a wasan bara da aka yi.

Labarai masu alaka