Nigeria za ta fafata da Honduras a Rio

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria ta taba lashe lamabar zinare a shekarar 1996

Tawagar kwallon kafa ta matasan Nigeria ta maza 'yan kasa da shekara 23 za ta kara da ta Honduras a gasar Olympic a ranar Juma'a.

Kasashen biyu za su kara ne a wasan neman mataki na uku, inda duk wadda ta samu nasara za ta karbi lambar yabo ta tagulla.

Nigeria ta yi rashin nasara a hannun Jamus da ci 2-0 a wasan daf da karshe, yayin da Honduras ta sha kashi da ci 6-0 a hannun Brazil.

Bayan sun kammala wasansu ne za a buga karawar karshe tsakanin Brazil da Jamus.