Pogba zai buga a karawa da Southampton

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pogba ne dan kwallon da aka saya mafi tsada a duniya a bana

Paul Pogba zai buga wa Manchester United wasansa na farko a gasar Premier da za ta fafata da Southampton a ranar Juma'a.

Pogba bai buga wa United wasan farko da ta ci Bournemouth 3-0 ba, sakamakon hukuncin dakatar da shi da aka yi a Juventus.

United ta sayo Pogba daga Juventus kan kudi fan miliyan 89, kuma shi ne dan wasan tamaula da aka saya mafi tsada a tarihi.

Pogba ya bar kulob din Manchester United a kan kudi fam miliyan daya da rabi a 2012.

Shi ma mai tsaron baya Chris Smalling ya kammala horon hana shi buga wasa daya, watakila ya maye gurbin Daley Blind.

Labarai masu alaka