Bolt ya lashe tseren mita 200 a Rio

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bolt zai yi wasan karshe a tseren mita 100 ta 'yan wasa hudu a ranar Lahadi

Usain Bolt ya lashe lambar yabo ta zinare a tseren mita 200, kuma ta takwas jumulla da ya ci a wasannin Olympic.

Dan kasar Jamaica, ya cinye tseren ne a dakika 19.78, dan kasar Canada Andre de Grasse ya yi na biyu, sai Christophe Lemaitre na Faransa ya kammala a na uku.

Bolt mai shekara 29, wanda tuni ya lashe zinare a tseren mita 100 a Brazil, zai kuma wakilci Jamaica a tseren mita 100 ta 'yan wasa hudu a wasan karshe a ranar Lahadi.

Shi ne wanda ya ci lambobin zinare a tseren mita 100 da 200 da kuma na 100 na 'yan wasa hudu a gasar da aka yi a Beijing da ta Landan.

Labarai masu alaka