'Yan Nigeria sun je Olympics ba kayan wasa

Olu Olamigoke Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan ciki har da Olu Olamigoke sun yi amfani da tsaffin kayansu ne

Wasu 'yan wasannin tsere na Nigeria a gasar Olympics da ake yi yanzu haka a Rio sun ce sai da aka yi kwanaki 13 da fara wasannin sannan aka basu kayan su na wasannin.

Da damansu dai sun kammala wasannin ne a lokacin da kayan su ka isa kasar ta Brazil.

Sun shaidawa BBC cewa wannan wani babban "abin kunya ne da ban mamaki, sannan suka ce sun yi amfani ne da tsofaffin kayansu ne".

Biyu daga masu tseren da suka nemi a boye sunayensu sun shaidawa BBC cewa sai ranar Alhamis suka karbi kayan wasan na su, bayan an fitar da su daga gasar.

Wani dan kwamitin wasannin motsa jiki na Nigeria ya ce bai taba ganin irin wannan abin kunya ba tun da yake a harkokin wasanni.

Wannan dai ya kara fito da abin kunyar da kasar ke fuskanta a wasannin na Olympics.

A baya ma sai da aka kai ruwa rana kan biyan kudin jigilar 'yan wasan kwallon kafa zuwa Brazil, abin da kuma ya janyo jinkirin zuwansu kasar.

Tawagar 'yan kwallon ta 'yan kasa da shekaru 23 ta isa ne 'yan sa'o'i gabanin wasansu na farko.

Har yanzu dai Najeriya ba ta kai ga samun lambar yabo ko daya ba a wasannin na bana.