Kanin Bello ya buge Shagon Sadam Hussain

Image caption A turmi na uku Ali Kanin Bello ya buge Shagon Sadam Hussain

Ali Kanin Bello ya buge Shagon Sadam Hussain a wasan damben gargajiya da suka fafata a ranar Lahadi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Ali Kanin Bello dan wasan Arewa ya samu nasara ne a kan Shagon Sadam Hussain daga Kudu a turmi na uku daf da za a rabu su wasa.

Alin ya sake yin wasa na biyu da Fatalwar Shagon Alabo, daga baya wasan ya zo da takaddama, inda Fatalwa ya ce Ali ya dafa kasa, amma alkalin wasa Shagon Amadi ya ce bai dafa ba.

Wasu daga cikin wasannin da aka yi Shagon Fijo daga Arewa ya doke Matawallen Kwarkwada daga Kudu a turmi na biyu.

Shi kuwa Shagon Hafsat daga Kudu buge Shagon Inda ya yi na Arewa a turmin farko, karawa tsakanin Shagon Sisko daga Kudu da Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa canjaras suka yi a tsawon turmi uku.

Damben Audu Dan Kirisfo daga Arewa da Sani Shagon Kwarkwada daga Kudu shi ma babu wanda ya je kasa.

Haka ma karawa tsakanin Autan Faya daga Kudu da Shagon Moyi 'yar Kaza daga Arewa suka tashi babu kisa.

Labarai masu alaka