Arsenal: Joel Campbell ya koma Sporting Lisbon

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Joel Campbell lokacin da ya kasa cin kwallo a gasar Kwallon Kafa ta Duniya ta 2014

Dan wasan Arsenal na gaba, Joel Campbell ya koma kungiyar wasa ta Sporting Lisbon da ke kasar Portugal.

Campbell din dai zai zauna a Lisbon ne har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Dan wasan mai shekara 24 ya kwashe shekara biyar a Arsenal amma kuma yana ta son ya koma babban kulob.

Ya ci wa Arsenal kwallaye hudu a wasanni 30 na kakar wasan da ta gabata.

Campbell, dan asalin kasar Costa Rica ya je kungiyoyi a kan aro kamar Lorient da Real Betis da Olympiakos da kuma Villareal.

Labarai masu alaka