Olympics: Niger ta fi Nigeria ƙoƙari

Hakkin mallakar hoto Getty Images Sports
Image caption Abdoulrazak Issoufou tare da dan wasan Taekwando na kasar Azerbajan.

Jamhuriyar Niger ta samu lambar yabo ta azurfa a gasar wasannin Olympics a birnin Rio.

Dan wasan kokawar Taekwondo, Abdoulrazaka Issoufou Alfaga ne ya ciyo wa kasar tasa lambar, bayan da ya doke dan kasar Azerbeijan, Radik Isaev, a wasan karshe na gasar, ranar Lahadi.

Alfaga ya samu nasara a kan dan wasan Faransa, Bar N'Diaye da na Brazil, Maicon Siquera da kuma dan Uzbekistan, Dimitri Shokin, a matakin wasan daban-daban.

Wannan dai shi ne karon farko da jamhuriyar Niger ta samu lambar yabo tun bayan tagulla da dan kasar, Issaka Daborg ya samu a gasar dambe a Munich a 1972.

Makwabciyar Niger din wato Najeriya dai ta samu tagulla ne kawai a wasan da ta yi da Honduras, a inda aka tashi 3-2.

Hakan na nufin Niger ta ɗara Najeriya a martabar lambar yabo.

Labarai masu alaka