Andy Carroll na West Ham zai yi jinya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwallaye tara ya ci a wasanni 27 da ya buga wa West Ham a bara

Dan wasan gaba na West Ham United, Andy Carroll, zai yi jinya tsakanin makonni hudu zuwa shida, bayan da ya yi rauni a gwiwarsa.

Dan kwallon mai shekara 27, ya yi rauni ne a karawar da kungiyarsa ta tashi kunnen doki 1-1 da Astra Giurgiu a wasan neman shiga gasar zakarun Turai ta Europa.

A farkon makonnan West Ham ta yi rashin Andre Ayew, wanda shi ma ya yi rauni a fafatawar da Chelsea ta ci West Ham 2-1 a gasar Premier, zai kuma yi jinyar makonni hudu.

Sauran 'yan kwallon West Ham da ke yin jinya sun hada da Aaron Cresswell da Sofiane Feghouli da kuma Manuel Lanzini.

Shi kuwa Dimitri Payet baya kan ganiyarsa, bayan hutu da ya yi, sakamakon gasar kofin nahiyar Turai da ya buga wa Faransa.

Labarai masu alaka