Benteke yana da banbanci da Messi — Delaney

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Christian Benteke ya koma Crystal Palace daga Liverpool

Dan wasan baya na Crystal Palace, Damien Delaney ya ce sabon dan wasan da kulob din ya saya, Christian Benteke yana bukatar taimako daga sauran abokan wasa domin shi ba Messi ba ne.

Delaney ya ce " Ba Messi muka siyo ba duk da dai shi ma dan wasa ne mai kyau amma dai ba dan wasan da zai samu kwallo ba ne kuma ya ci duka shi kadai."

Ya kara da cewa " dole ne mu taimaka masa da buga masa kwallo."

Benteke, mai shekara 25 dai ya koma Crystal Palace ne daga Liverpool akan tsabar kudi har £27m.

Labarai masu alaka