Claudio zai je gwajin lafiya a Man City

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Golan Man City, Joe Hart yana cikin zulumi kan zuwan Claudio Bravo kulob din.

Golan Barcelona, Claudio Bravo zai je Manchester City domin gwajin lafiyarsa.

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ne dai ya nemi Bravo dan kasar Chile, mai shekara 33 domin ya zama mai tsare wa kulob din raga, lamba daya.

Guardiola ya ce " ba zan boye abin da mutane suka sani ba. Ba a kammala yarjejeniyar ba tukunna saboda haka bai zama namu ba."

Idan dai har aka kammala yarjejeniyar to Joe Hart zai zama jeka-na-yi-ka a kulob din.

Labarai masu alaka