FA ta dakatar da gola kan kalaman batanci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Scott Flenders ya fadi kalaman batanci ga wasu

Hukumar Kwallon Kafar Ingila ta FA ta dakatar da golan York City, Scott Flinders har na tsawon wasanni biyar, bayan an same shi da laifin nuna wariyar launin fata.

An kuma ci tarar sa £1,250 sannan kuma hukumar ta wajabta masa yin wani kwas.

An dai ce Scott Flinders ya yi amfani da kalaman batanci da kuma zagi wadanda sun saba doka.

Al'amarin dai ya faru ne a lokacin wasan da su kyi da AFC Wimbledon a ranar 19 ga Maris.

Dan wasan, mai shekara 30 bai amince da tuhumar da ake yi masa.

Labarai masu alaka