FA tana tuhumar dan wasa kan sukar Luwadi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andre Gray ya nemi afuwa kan cewa kisan masu luwadi ba laifi.

Hukumar Kwallon Kafar Ingila, FA ta tuhumi dan wasan Burnley, Andre Gray da laifin nuna kyamar 'yan neman maza a wani bayani da ya wallafa a shafinsa na Twitter a 2012.

Gray ya wallafa bayanin ne tun bai fara buga wasannin Premier ba.

Bayanin da dan wasan ya wallafa dai ya nuna cewa kisan 'yan luwadi ba laifi ba ne.

Yanzu haka, dai hukumar ta FA ta ba wa Gray din har zuwa karfe shida na yamma na ranar 31 ga watan Agusta, da ya bayar da bahasi.

Tuni dai ya nemi afuwa dangane da bayanan nasa da ya wallafa, a inda yake cewa shi yanzu "mutum ne wanda ya sauya halinsa," sannan kuma "bai yi imani da abin da ya rubuta ba."

Labarai masu alaka