Joe Hart zai tsare ragar Man City

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Joe Hart dai zai zama gola mai matsayi na biyu idan Claudio Bravo ya zo Man City

Yanzu haka dai ta bayyana cewa golan Manchester City, Joe Hart zai tsare ragar kulob din karon farko a wannan kakar wasannin.

Manchester City dai za ta taka leda ne da Steaua Bucharest ranar Laraba, a wasan zagaye na biyu na gasar Zakarun Turai ta Champions League.

Shi dai Joe Hart mai shekara 29 bai tsare wa Man City raga ba ko da sau daya a wannan kakar wasannin.

Kuma kocin kulob din Pep Guardiola ya fada masa cewa yana da zabin cigaba da zama ko barin kungiyar.

Golan Barcelona, Claudio Bravo, mai shekara 33 na gab da zuwa Man City domin yi masa gwajin lafiya.

Labarai masu alaka