'Hana Russia gasar Paralympics ya yi dai-dai'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A watan Satumba ne za a fara gasar Paralympics

'Yan wasan Russia ba za su shiga wasan Olympics na nakasassu ba da za a yi a wata mai kamawa, a birnin Rio na Brazil, bayan rashin nasara a karar da kasar ta daukaka kan dakatarwa da aka yi mu su.

Hukumar Kula da Wasannin Paralympics ta Duniya, IPC ce dai ta dakatar da 'yan wasan Russia bisa laifin rufa-rufa wajen boye sakamakon gwajin shan kwayoyi masu kara kuzari da aka yi wa 'yan wasan na Russia.

Kotun Hukunta Laifuka kan Wasanni ta (Cas) ta amince da hukuncin da hukumar ICP ta dauka na dakatar da Russia daga wasannin.

ICP dai ta dauki matakin dakatarwar ne bisa la'akari da rahoton McLaren wanda ya bayyana yadda badakalar gwajin da aka yi wa 'yan wasan na Russia ta faru.

Za a dai a fara wasannin Olympics na nakasassun ne ranar 7 ga Satumba.

Labarai masu alaka