Premier: Sunderland za ta iya sake faɗowa — Moyes

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kocin Sunderland, David Moyes

Kocin Sunderland, David Moyes ya ce gaskiya ya fada a lokacin da ya fada wa magoya bayan kulob din su shirya yakin sake fadowa daga teburin gasar Premier ta bana.

Sunderland dai ta sha yin kokarin hawa saman teburin gasar, a kakar wasanni hudu da suka gabata amma hakan bai samu ba.

A wannan kakar kuma kulob din bai samu nasara ba a wasanni biyu na farkon gasar ta Premier kuma Sunderland din ce ta 18 a teburin gasar.

Moyes ya ce " na fada cewa ina son kawo sauyi amma kuma ba zan iya yin hakan ba a lokaci guda."

Labarai masu alaka