AC Millan ta hana Romagnoli zuwa Chelsea

Image caption Alessio Ramagnoli ya je AC MIllan daga Roma

AC Millan ta yi watsi da tayin da Chelsea ta yi a kan dan wasan baya na kulob din, Alessio Romagnoli, sannan kuma ta kara da cewa dan wasan ba na siyarwa ba ne.

Rahotanni dai sun ce Chelsea dai ta taya dan wasan mai shekara 21 a kan kudi £35m.

Ramagnoli wanda dan kasar Italiya ne ya je AC Milan ne daga Roma a kan £21.25m, a bazarar da ta gabata.

Wata sanarwa da aka fitar a shafin intanet na dan wasan ta ce "dan wasan ba na sayarwa ba ne saboda haka babu batun tattaunawa kan dan wasan."

Ramagnoli dai ya fara fitowa a gasar Serie A ta Italiya a lokacin yana da shekara 17 kuma ya buga manyan wasanni sau 77 ga Roma da Milan da kuma Sampdoria.

Kawo yanzu dai, kocin Chelsea, Antonio Conte ya samu nasarar daukar dan wasan tsakiya na Leicester N'golo Kante da dan wasan Marseille na gaba, Michy Batshuayi.

Labarai masu alaka