Arsenal da Everton na takara kan Lucas

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana tunanin dai Arsenal ne ce za ta samu nasarar sayen Perez

Kulob din Arsenal ya kudiri niyyar shiga takara da Everton wajen zawarcin dan wasan Deportivo La Coruna, Lucas Perez Martinez, a kan kudi £17m.

Everton dai tana son sayen dan wasan mai shekara 27 wanda ya zura kwallaye 17 a gasar La Ligar da ta gabata, domin taimaka wa Romelu Lukaku.

To amma kwatsam sai Arsenal ita ma ta bayyana bukatarta ta sayen dan wasan.

Har yanzu kuma Everton din ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen neman dan wasan duk da rahotanni daga Spaniya sun nuna cewa kulob din Arsenal ne a gaba-gaba wajen samun dan wasan.

Kocin Everton, Ronald Koeman da darektan kulob din Steve Walsh ba za su ji dadi ba kasancewar kulob din nasu ne ya fara nuna sha'awar daukar dan watan.

Har wa yau dai ana alakanta Everton da neman dan wasan Napoli, Manolo Gabbiadini.

Labarai masu alaka