Barcelona ta sayi golan Ajax

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jasper Cillessen ya fara wasan kwallo ne a NEC Breda

Jasper Cillessen, mai shekara 27 wanda dan kasar Netherlands ne zai zauna a Barcelona ne na tsawon shekara biyar.

Golan dai ya fara wasa ne tare da NEC Breda kafin ya koma Ajax a 2011.

Wannan dai na zuwa ne 'yan awowi kafin Claudio Bravo ya koma Manchester City a kan kudi £15.4m.

Labarai masu alaka