Burina na yi ritaya a Man United — Bastian

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bastian Schweinsteiger a lokacin gasar Euro 2016

Dan wasan Manchester United na tsakiya, Bastian Schweinsteiger ya ce kulob din ne wurin da zai taka leda na karshe a Tarayyar Turai kuma a "shirye na ke da hakan idan Man United din na bukata."

Dan wasan, mai shekara 32 dai ya taka wasanni guda 31 a kakar wasannin da ta gabata.

Bastian ya kasance yana atisaye shi kadai da kuma tare da 'yan kasa da shekara 21 tun lokacin da Jose Mourinho ya karbi ragamar horas da 'yan wasan kulob din.

A watan Yulin 2015 ne dai dan wasan ya rattaba hannu a kan kwantaragin zama a Man United na shekara uku, a karkashin Louis van Gaal.

Schweinsteiger ya yi murabus daga buga kwallon kasa da kasa bayan gasar Euro 2016.

Labarai masu alaka