Tottenham ta ba wa Schalke aron Bentaleb

Image caption Nabil Bentaleb zai zauna a Schalke zuwa karshen kakar wasanni

Dan wasan tsakiya na Tottenham, Nabil Bentaleb ya koma kungiyar wasa ta Schalke da ke Jamus, domin takawa kulob din leda a kakar wasannin bana.

Dan wasan, dan asalin kasar Algeria mai shekara 21 ya je Tottenham yana matashi, a inda kuma ya fara buga wasa a watan Disamban 2013.

Ya buga wasanni a kulob din har sau 66 amma kuma har yanzu bai buga wasa ba a wannan kakar karkashin Mauricio Pochettino.

Kulob din na Schalke dai wanda ya zo na biyar a teburin gasar Bundesliga ta Jamus, yana gab da sayen tsohon dan wasan Tottenham, Benjamin Stambouli daga PSG.

Labarai masu alaka