Drinkwater zai ci gaba da zama a Leicester

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Danny Drinkwater ya amsa kiran Claudio Ranieri cewa 'yan wasan su tsaya a kulob din har zuwa wata kakar.

Dan wasan Leicester na tsakiya, Danny Drinkwater ya rattaba hannu a kan sabon kwantaragin cigaba da zama a kulob din na tsawo shekara biyar.

Dan wasan mai shekara 26 na daya daga cikin 'yan wasan da suka taimaka har kulob din ya dauki kofin Premier.

Kwantaraginsa na asali dai zai kare ne a 2018 kuma ana ta rade-radin cewa zai koma Tottenham da taka leda.

Kocin kulob din, Claudio Ranieri da wasu daga cikin abokan wasansa da suka hada da Riyad Mahrez da Jamie Vardy da Kasper Schmeichel da Wes Morgan da kuma Andy King duka sun sabunta kwantaraginsu a kulob din.

Drinkwater ya ce " ina son taka wa kulob din leda domin ya matukar dacewa da ni kuma zan so na ci gaba da kasancewa a kulob din har wani tsawon lokaci."

Labarai masu alaka