Zan yi koyi da magabata -— Klopp

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A 2015 dai Jurgen Klopp ya je Liverpool

Kocin Liverpool ya ce yana fatan dorawa a kan yadda magabatan kociyoyin kulob din suka gina shi.

A watan Octoban 2015 ne dai aka nada Klopp, mai shekara 49 a matsayin kociyan Liverpool kuma ya jagoranci kulob din har ya kai mataki na takwas a teburin gasar Premier.

Kuma ya jagoranci kulob din zuwa wasan karshe na gasar League Cup da Europa League.

Klopp dai yana son dorawa ne a kan ayyukan da magabatansa kamar Bill Shankly da Bob Paisley suka yi.

Jurgen ya ce " wani lokacin kana bukatar koyi daga basirar mutanen da suka gabace ka."

Labarai masu alaka