Man City ta sayi golan Barcelona a kan £15.4m

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Claudio Bravo ya je Barcelona daga Ajax

Manchester City ta sayi golan Barcelona, Claudio Bravo, mai shekara 33, a kan £15.4

Bravo wanda dan kasar Chile ne zai zama gaba da Joe Hart da Willy Caballero.

Wannan dai na zuwa ne kwana daya bayan da Joe Hart ya taka wasansa na farko a wannan kakar wasannin.

Barcelona dai ta maye gurbin Bravo da dan kasar Neitherland, Jasper Cillessen wanda ya je kulob din daga Ajax.

Bravo dai ya je Barcelona ne a 2014, a inda ya taimaka wajen lashen kofin gasar La Liga har guda biyu.

Da shi ne kuma kulob din ya yi nasarar a gasar Champions League da kuma ta Wasan Kwallon Kafa na Duniya.

Labarai masu alaka