Greg Clarke ya zama shugaban FA

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Greg Clarke tsohon shugaban Hukumar Gasar League ne

Tshohon shugaban Kungiyar Gasar Kwallon League ta Ingila, Greg Clarke ya maye gurbin Greg Dyke a matsayin shugaban Hukumar Kwallon Kafar Ingila.

Clarke wanda tsohon shugaban Leicester City ne, ya bar mukaminsa na shugabancin Kungiyar Gasar League din a watan Yuni.

A watan da ya gabata ne dai aka zabe shi domin maye gurbin Dyke kuma yanzu haka majalisar hukumar ta FA ta amince da nadin.

Greg Clarke zai shiga ofis a ranar 2 ga watan Satumba.

Labarai masu alaka