Newcastle ta sayi DeAndre Yedlin

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Newcastle ta sayi 'yan wasa 9 a wannan bazarar.

Newcastle United ta sayi dan wasan Tottenham, DeAndre Yedlin a kan kwantaragin shekara biyar, a kan kudin da ba a bayyana yawansu ba.

Yelin, mai shekara 23, ya kwashe tsawon kakar wasannin da ta gabata a Newcatle United a aro, a inda ya buga wasanni har sau 25.

Yelin dai zai maye gurbin Daryl Janmaat wanda ya koma Watford.

Dan wasan ya zama mutum na tara da kocin kungiyar, Rafael Banitez ya saya a wannan kakar bazarar.

Labarai masu alaka