Euro 2017: Rashford zai buga wa England wasa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Marcus Rashford a lokacin wasan Ingila da Wales

Dan wasan Manchester United na gaba, Marcus Rashford na cikin jerin sunayen 'yan wasa 'yan kasa da shekara 21 da za su buga wa Ingila wasan neman gurbin shiga gasar Euro 2017.

Ingilar dai za ta kara da Norway a ranar 6 ga watan Satumba.

A gasar Euro 2016, Rashford dai ya maye gurbin wasu 'yan wasa a wasannin har sau biyu.

Wannan ne karon farko da Rashford zai buga wasannin 'yan kasa da shekara 21.

Rashford dai shi ne dan wasa mafi karancin shekaru da ya ci wa Ingila kwallo a wasansa na farko wanda suka yi da Australia, a watan Mayu.

Marcus ya kuma ci wa Manchester United kwallaye har guda takwas a wasanni 18 a kakar wasa da ta gabata duk da dai har yanzu bai taka leda ba a karkashin sabon kociya, Jose Mourinho.

Labarai masu alaka