Rio 2016: Rawar ganin da Afirka ta taka

Nahiyar Afirka ta taka gagarumar rawa a gasar wasannin Olympics da aka yi a birnin Rio na Brazil. Ga wasu mahimman abubuwa da ba za a taba mantawa da su ba.

  • Dan wasan tseren ya-da-kanen-wani na Afirka ta Kudu, Wayde van Niekerk ya samu lambar yabo ta Zinare bayan da ya zo na daya a gudun mita 400, a karon farko, tun bayan da Machael Johnson ya yi bajintar a 1999.

Yanzu haka shi ne mai rike da kambun gwarzon dan tseren gudun na mita 400, a duniya.

  • Kenya ce ta zama ta 15 a cikin kasashe 78 da suka samu lambar yabo a gasar ta Rio. Kasar dai tana da lambobin yabo guda 13 a inda shida daga ciki Zinare ne. Afirka ta Kudu ce take biye mata baya, sai kuma Ethiopia. Ivory Coast ce kuma ta hudu a Afirka bayan da ta samu lambar yabo ta Zinare a karon farko.
  • A lokacin wasannin na Olympics a Rio, mutane sun yi ta mamakin yadda dan wasan tseren keke na Namibia, Dan Craven yake wallafa bayanai ta shafinsa na Twitter alhali yana kan gudu a keke.

To amma daga baya ta bayyana cewa budurwarsa ce take wallafa bayanan ba dan wasan ba.

  • Dan wasan tseren fanfalaki na kasar Ethiopia, wanda ya ciyo wa kasar lambar yabo, Feyisa Lelisa ya daga hannayensa sama, a inda ya ratsa daya kan daya wanda kuma hakan alamun nuna goyon baya ne ga al'ummar Oromo wadda kabilarsa ce.

Shi kuma ya yi hakan ne domin ya yi Alla-wadai da farmakin da 'yan sanda suka kai wa 'yan kabilar. Hakan kuma kamar sukar gwamnatin kasar ne.

Shi Feyisa ya ce yana tsoron komawa gida saboda za a hukunta shi. Take kuma a birnin na Rio aka fara hada gidauniyar tara kudade domin nema masa mafaka a wata kasar.

Hakkin mallakar hoto Getty
  • Matan Afirka da suka dauki lambobin yabo: Sara Ahmed ce ta zama macen farko 'yar Misra da ta fara lashe lambar yabo ta Tagulla a wasan daga nauyi.

Sara dai ta hakura da zana jarrabawa domin ta samawa kasar tata lamba kuma ma'aikatar ilimin Misra taki yarda ta daga mata kafa domin ta zana jarrabawar daga baya.

Hedaya Wahba, 'yar kasar Misra ce kuma macen farko da ta lashe lambar yabo a damben Taekwondo.'Yar kasar Tunisia, Ines Bounakri, ita ma ta samu lambar yabo a wasan kokawar.

  • Wani likitan fida dan kasar Japan, Katsuya Takasu ya yi takakkiya daga birnin Tokyo zuwa Rio domin ya ba wa 'yan wasan Najeriya kyautar kudi har dalar Amurka 390,000 saboda irin bajintar da 'yan wasan suka nuna sakamakon lashe lambar yabo ta Tagulla, bayan doke Honduras da ci 3-2 a wasan neman matsayi na uku.

Labarai masu alaka