Javier Manquillo ya koma Sunderland

Hakkin mallakar hoto Liverpoolfc
Image caption Javier Manquillo a lokacin da ya je Liverpool a kan aro

Sunderland ta sayi dan wasan baya na Atletico Madrid, Javier Manquillo a kan yarjejeniyar aro domin takawa kulob din wasa a wannan kakar.

To amma Sunderland din tana da damar mayar da kwantaragin ya zuwa na dun-dun-dun, a karshen kakar wasannin ta bana.

Javier, mai shekara 22, ya je Liverpool domin taka musu leda a yarjejeniyar aro a kakar wasa ta 2014-2015.

Bayan kuma ya bar Liverpool ne, ya je kulob din Marseille a kakar wasan da ta gabata, a inda ya buga wasanni har 43ya kuma zura kwallaye uku.

Labarai masu alaka