West Ham na zawarcin Bony

Hakkin mallakar hoto manchester city
Image caption Wilfried Bony ya je Man City a 2015

Kocin West Ham, Slaven Bilic ne ya ce yana son sayen dan wasan gaba na Manchester City, Wifried Bony.

'Yan wasan gaba na West Ham dai guda biyu, Andy Carroll da Andre Ayew duka sun samu rauni.

Hakan ne ya sa Bilic yake son cike gurbin da kulob din ya samu.

Bilic ya ce yana zawarcin Bony dan kasar Ivory Coast saboda shi ma dan gaba ne.

Wifried Bony dai ya je Manchester City a watan Janairu na 2015 kuma ya zura kwallaye 10 a wasanni 20.

Sai dai kuma a wannan kakar, har yanzu bai kai ga zura kwallo ko da guda daya ba.

Labarai masu alaka