Watford ta sayi Daryl Janmaat

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Daryl Janmaat a cikin tawagar 'yan Hollande

Watford ta sayi dan wasan Newcastle na baya Daryll Janmaat kan kwantaragin shekara hudu a kan kudi £7.5m.

Dan wasan mai shekara 27 dai ya kwashe kakar wasanni guda biyu a Newcastle din, a inda ya ci kwallaye guda hudu a wasanni 77.

Sai dai kuma Janmaat bai buga wasa ba a wasanni ukun da kungiyar ta taka a gasar Championship.

Watakila dan wasan ya fara buga wasansa na farko a Watford, a wasan da kulob din zai taka da Arsenal, ranar Asabar.

Labarai masu alaka