Joseph Yobo zai koma Kano Pillars

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Joseph Yobo a lokacin da ya ci gidansa Najeriya

Shirye-shirye sun kankama na komawar tsohon kyaftin din kungiyar wasa ta kasar, Joseph Yobo zuwa kungiyar wasa ta Kano Pillars.

Wata majiya a Kano Pillars ta shaida wa BBC cewa Hukumar Kula da Wasannin Premier League ta kasar wato NPFL ta amince da shirin.

Hukumar ce dai ta nada Joseph Yobon a matsayin jakadanta, hakan ne yasa dan wasan zai je Pillars din ya taka leda domin ya amsa sunan mukamin nasa.

Sai dai kuma rahotanni na cewa bayan Kano Pillars akwai wasu kungiyoyi guda uku da suka hada da Akwa United da Ifeanyi Ubah FC da Wikki Tourists da su ma suke zawarcin Yobo.

Joseph Philip Yobo wanda tsohon dan wasan baya ne na Everton da Fenerbahce, ya yi murabus daga buga kwallon kasa da kasa a 2014.

Labarai masu alaka