An rusa kwamitin Olympic na kasar Kenya

Hukumomi a Kenya sun rusa kwamitin da ke kula da 'yan wasan Olympic na kasar (NOCK).

Ministan wasanni na Kenya, Hassan Wario, wanda ya bayyana haka a wurin wani taron manema labarai da aka yi a Nairobi babban birnin kasar, ya ce an rusa NOCK ne domin a samu damar yin bincike a kan rashin bayar da kyakkyawar kulawa ga tawagar Kenya a gasar Olympics da aka kammala kwanan nan a Rio de Janeiro.

A ranar Laraba ne dai masu bincike suka yi wa minista Wario da kanshi tambayoyin kwakwa game da rashin bai wa tawagar Kenya kulawar da ta dace, lamarin da ya sa kasar ta yi kaurin suna gida da waje a lokacin wasannin na Olympic da aka yi a kasar Brazil.

Rusa kwamitin na NOCK ya zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke fitowa na cewa wasu 'yan wasan Kenyan sun makale a Rio de Janeiro bayan an kammala wasan olympics din a ranar Laraba.

Labarai masu alaka