An hana Wellington bizar Faransa

Gwarzon wasan scrabble na duniya a yanzu, Wellington Jighere ya ce an hana shi tare da 'yan tawagarsa bizar zuwa kasar Faransa domin su shiga gasar wasan Scrabble.

Wellington ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook inda ya ce " an hana ni tare da tawagata 'yan Nigeria biza. Haka maganar ta ke, dai-dai kuka ji. An hana kasar da ta ke kan gaba a duniya a wasan scrabble izinin shiga Faransa domin shiga gasar."

A watan Nuwamba ne dai Wellington Jighere ya zamo dan Afirka na farko da ya yi nasarar gasar wasan scrabble a harshen turanci na duniya.

Labarai masu alaka