Kenya: An cafke 'yan kwamitin Olympics

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kenya ta fi kowace ƙasa a nahiyar Afrika samun lambar yabo a gasar Olympics ta Rio.

A ƙasar Kenya, an tsare wasu jami'ai na kwamitin gasar wasannin Olympic a Nairobi bisa zargin su da hannu a wata badakala a lokacin wasan Olympics da aka kammala a Rio.

Jami'an 'yan sanda sun ce za'a tuhumi sakatare janar na kwamitin Francis Paul da kuma wasu mutum biyu ranar Litini.

Kenya dai ta ƙaddamar da bincike kan matsalolin da 'yan wasan ta suka fuskanta a lokacin gasar wadanda suka hada da rudani wajen shirye shirye da bacewar kayayyakin 'yan wasa da kuma batun shan kwayoyi masu ƙara kuzari.

A ranar Alhamis ne dai ministan wasanni na ƙasar ya rusa kwamitin sai dai kuma mambobin kwamitin sun ƙi su bar aiki.

Kenya ce ta fi kowace ƙasa a nahiyar Afrika samun lambar yabo a gasar ta Rio.

Labarai masu alaka