Za a yi gyara a kwallon kafar Olympics

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana yin wasan kwallon kafa ta maza da ta mata a Olympic

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino, na son a yi gyararraki a kan muhimman abubuwa a wasan kwallon kafa da ake yi a Olympic.

Shugaban ya ce ya kamata a yi duba na tsanaki a wasannin maza na matasa 'yan kasa da shekara 23 wanda ake kara 'yan wasa uku da suka haura shekarun da cewar hakan ba shi da wani amfani.

Infantino ya kuma ce wasannin da ake yi ba sa cikin jadawalin wasannin Fifa, wanda hakan ke sa wasu kungiyoyin ke hana 'yan wasansu zuwa gasar.

Tawagar kasashe 16 ne ke shiga gasar kwallon kafa ta maza da ake yi a Olympics, inda Brazil ta lashe ta Rio da aka yi a kasarta.

Haka kuma kasashe 12 suke fafatawa a gasar kwallon kafar ta mata, inda Jamus ta lashe lambar zinare a gasar Rio.

A shekarar 2008 ne Barcelona da Werder Bremen da Schalke suka samu nasara a kan karar da suka shigar cewar ba lallai ba ne su bar 'yan wasansu su je gasar, domin wasannin ba sa cikin jadawalin Fifa.

Labarai masu alaka