Joao Mario ya koma Inter Milan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Joao Mario dan wasan tawagar kwallon kafa ta Portugal

Inter Milan ta dauki Joao Mario daga Sporting Lisbon kan kudi fan miliyan 38.4, wanda hakan ya sa ya zama dan kwallon Portugal da wata kungiya daga kasar ta sayar mafi tsada a tarihi.

Dan kwallon mai shekara 23, ya dara kudin da Sporting ta sayar da Cristiano Ronaldo fan miliyan 12.24 da kuma Nani fan miliyan 25 ga Manchester United.

Haka kuma shi ne dan wasa na biyu mafi tsada da aka saya daga Portugal, bayan James Rodriguez na Colombiya da Monaco ta saya daga Porto a shekarar 2013.

Mario mai wasan tsakiya, ya yi wa Sporting wasanni sau 171, ya kuma buga wa kasarsa dukkan karawar da ta yi ta lashe kofin nahiyar Turai da aka yi a Faransa.

Inter Milan din tana kuma tattaunawa kan batun dauko Gabriel Barbosa daga Santos.

Labarai masu alaka