Man City ta doke West Ham 3-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester City ta cinye wasanninta uku da ta buga a gasar ta Premier

Manchester City ta ci gaba da taka rawar gani a gasar Premier bana, bayan da ta ci West Ham United 3-1 a wasan mako na uku da suka kara a gasar a ranar Lahadi.

City ce ta fara cin kwallo ta hannun Raheem Sterling, sannan Fernandinho ya kara ta biyu da ka kafin aje hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne daga hutu West Ham ta ci kwallo daya da ka ta hannun Michail Antonio, bayan da Arthur Masuaku ya bugo masa tamaula.

Daf da za a tashi ne daga fafatawar Sterling ya ci wa City kwallo na uku kuma na biyu da ya zura a ragar West Ham.

Labarai masu alaka