Aguero ba zai buga wa Argentina kwallo ba

Sergio Aguero ba zai buga wa Argentina wasan neman shiga gasar kofin duniya ta 2018 ba, sakamakon raunin da ya yi.

Hukumar kwallon kafa ta Argentina ce ta sanar da raunin da dan kwallon ya yi a lokacin da ya buga karawar da Manchester City ta doke West Ham 3-1 a gasar Premier a ranar Lahadi.

Tawagar Argentina za ta kara da ta Uruguay a ranar Juma'a, sannan ta fafata da Venezuela a ranar 7 ga watan Satumba.

Lionel Messi na yin atisaye da tawagar Argentina bayan da aka rarrasheshi ya janye ritayar da ya ce ya yi daga buga wa kasar tamaula a farkon watan August.

Argentina tana mataki na uku a kan teburi, bayan da ta ci wasannin uku daga guda shida da ta yi.

Labarai masu alaka