Liverpool ta sayar da Luis Alberto

Hakkin mallakar hoto rex features
Image caption Luis Alberto ya buga tamaula aro a gasar Spaniya da aka kammala

Liverpool ta amince ta sayarwa da Lazio, Luis Alberto, kan kudi fan miliyan 4.3.

Alberto mai shekara 23, ya yi wa Liverpool wasanni 12, tun komarsa Anfield daga Sevilla kan kudi fan miliyan 6.8 a shekarar 2013.

Dan kwallon wanda ya yi wasanni aro a Deportivo La Coruna a bara, ya isa birnin Rome domin karasa cimma yarjejeniya.

Tsohon kociyan Liverpool, Brendan Rodgers ne ya sayo dan kwallon a lokacin.

Labarai masu alaka