Joe Hart na daf da komawa Torino

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hart bai buga wa City wasan Premier ba a bana

Mai tsaron ragar Manchester City, Joe Hart, na daf da shirin komawa Torino ta Italiya da murza-leda.

Koci Pep Guardiola ne ya shaidawa Hart mai shekara 29, cewa zai iya komawa wata kungiyar da wasa.

Kociyan Everton, Ronald Koeman, ya karyata rade-radin da ake yi cewar Hart zai koma can da taka-leda.

Har yanzu Hart bai buga wa City wasan Premier ba, karkashin koci Guardiola, wanda ya sayo golan Barcelona Claudio Bravo.

Labarai masu alaka