Wikki ce ta daya a kan teburin gasar Nigeria

Hakkin mallakar hoto LMC Facebook
Image caption An kammala wasannin mako na 33 a gasar Firimiyar Nigeria

Wikki Tourist ce ke jagorantar teburin gasar Firimiyar Nigeria, bayan da aka kammala wasannin sati na 33 a makon da ya wuce.

Wikki wadda take da kwantan wasa daya da Enyimba tana da maki 53 a wasanni 32 da ta yi, inda ta ci 15 ta yi canjaras a karawa takwas aka kuma doke ta sau takwas.

Rivers United ce a matsayi na biyu ita ma da maki 53, sai Ifeanyiubah wadda ke matsayi na uku da maki 52.

Kano Pillars wadda ta yi rashin nasara a hannun Shooting Stars da ci 4-0 a ranar Lahadi, tana mataki na 10 a kan teburin da maki 45.

Warri Wolves da Ikorodu United da kuma Giwa FC sune ke kasan teburin gasar Firimiyar Nigeria ta bana.

Labarai masu alaka