Gyan zai koma Reading buga tamaula aro

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Asamoah Gyan kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Ghana

Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Ghana, Asamoah Gyan, na daf da komawa Reading da murza leda a matsayin aro daga Shanghai SIPG ta China.

Dan wasan mai shekara 30, tsohon dan kwallon Sunderland ya isa Reading mai buga gasar Championship domin a duba lafiyarsa.

Gyan ya ci wa Sunderland kwallaye 10 a lokacin da ya buga mata wasanni shekara biyu daga 2010 kafin ya koma Al-Ain ta hadaddiyar Daulal Larabawa da taka-leda.

Daga nan ne ya koma Shanghai da wasa a shekarar 2015 a matsayin wanda aka saya mafi tsada a duniya a lokacin.

Labarai masu alaka