Arsenal ta dauki Perez daga Deportivo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A tsakar daren Laraba ne za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon a Turai

Arsenal ta dauki Lucas Perez daga Deportivo La Coruna kan kudi fan miliyan 17.1.

Dan kwallon tawagar Spaniya, wanda bai fara buga mata tamaula ba, ya ci wa Deportivo kwallaye 17 a wasanni 37 da ya yi, tun lokacin da ya koma Spaniya daga PAOK ta Girka.

Arsenal na dab da sanar da daukar dan wasan Valencia, Shkodran Mustafi kan kudi fan miliyan 35.

Tun farko Arsene Wenger ya sayi 'yan wasan tsakiya Granit Xhaka da Kelechi Nwakali da mai tsaron baya Rob Holding da mai cin kwallaye a bana.

Labarai masu alaka