Barcelona ta sayi Paco Alcacer

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona ta sayi 'yan wasa shida a bana kenan

Barcelona ta sayi Paco Alcacer daga Valencia kan kudi fan miliyan 30, kan yarjejeniyar shekara biyar.

Alcacer mai shekara 23, ya ci wa Valencia kwallaye 30, ya kuma zama kyaftin din kungiyar karkashin jagorancin Gary Neville a bara.

Alcacer shi ne dan wasa na shida da Barcelona ta dauka a bana, bayan mai tsaron raga Jasper Cillessen da masu tsaron baya Lucas Digne da Samuel Umtiti da masu wasan tsakiya Andre Gomes da kuma Denis Suarez.

Barcelona wadda ke rike da kofin La Liga na bara ta cinye wasannin biyu da ta buga a gasar bana.

Labarai masu alaka