Palace ta dauki Remy aro daga Chelsea

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Loic Remy dan kwallon kafar tawagar Faransa

Crystal Palace ta dauki Loic Remi daga Chelsea domin ya buga mata wasanni aro zuwa karshen kakar bana.

Remy dan wasan tawagar Faransa, ya buga wa Chelsea wasanni tara a shekara biyu da ya yi a Stamford Bridge tun komawarsa can daga QPR kan kudi sama da fan miliyan 10.

Dan kwallon ya buga tamaula karkashin koci Alan Pardew aro a Newcastle United a kakar shekarar 2013/14, inda ya ci kwallaye 14.

Tottenham kuma ta hakura da zawarcin Wilfred Zaha na Crystal Palace, bayan da kungiyar ta ki sayar mata da dan kwallon.

Labarai masu alaka