Rooney zai yi ritaya daga Ingila bayan 2018

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rooney zai ci gaba da buga wa United tamaula bayan ya yi ritaya daga Ingila

Kyaftin din tawagar Ingila, Wayne Rooney zai yi ritaya daga buga wa kasar tamaula bayan an kammala gasar cin kofin duniya a shekara 2018 da za a yi a Rasha.

Rooney ya fadi hakan ne a lokacin da 'yan jarida ke yi masa tambayoyi bayan da kociyan tawagar Ingila, Sam Allardyce ya ce dan wasan ne zai ci gaba da zama kyaftin din tawagar.

Rooney kyaftin din Manchester United ya buga wa tawagar Ingila wasanni 115, ya kuma ci mata kwallaye 53, shi ne dan wasan da ya fi ci wa kasar kwallaye.

Ingila ba ta taba kasa zuwa kofin duniya ba tun gasar 2009, sai dai rabon da ta haura wasan zagayen farko a gasar kofin duniya tun shekarar 2006 da aka yi a Jamus.

Labarai masu alaka