An tuhumi Aguero da laifin yin gula

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lokacin da Sergio Aguero ya yi wa Winston Reid gula a filin wasa

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi Sergio Aguero na Manchester City da laifin nuna halin rashin da'a, a wasan Premier da suka yi da West Ham United, a ranar Lahadi.

Hukumar ta tuhumi Aguero da laifin yi wa Winston Reid gula a karawar da City ta doke West Ham 3-1, a wasan Premier mako na uku.

Za a iya hukunta dan kwallon tare da hana shi buga wasanni uku, ciki har da fafatawar da City za ta yi da Manchester United ranar 10 ga watan Satumba, da karawa da Bournemouth ranar 17 ga watan mai kamawa.

Haka kuma Aguero mai shekara 28, ba zai buga wasan da kungiyarsa za ta yi da Swansea a gasar Capital Cup ba, idan har an same shi da laifi.

Hukumar ta bai wa dan wasan zuwa ranar Laraba domin ya kare kansa.

Labarai masu alaka