Somalia: Bam ya tashi dab da fadar shugaban kasa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan al-shabab dai sun yi mubaya'a da kungiyar al-Qaeda

Wata mota dauke da bama-bamai ta tarwatse a wajen wani otal da ke Mogadishu, babban birnin Somalia.

Har wa yau, otal din yana dab kofar shiga fadar shugaban kasa.

Akalla mutane biyar ne suka mutu kuma wani wanda ya shaida yadda al'amarin ya faru ya fada wa BBC cewa mutane da dama sun jikkata.

Tuni kungiyar al-Shabab mai alaka da al-Qaeda ta dauki alhakin kai harin.

Otal din mai suna Somali Youth League ya kasance sanannen wurin haduwar jami'an gwamnati kuma wannan ba shi ne karon afrko ba da aka kai masa hari.

Labarai masu alaka